Wednesday, March 18
Shadow

Duk Labarai

Dalibai ‘yan mata na jihar Kebbi Duk Musulmai ne, Karanta Jadawalin sunayensu

Dalibai ‘yan mata na jihar Kebbi Duk Musulmai ne, Karanta Jadawalin sunayensu

Duk Labarai
Hukumomi a jihar Kebbi sun musanta kalaman da wani ɗan majalisar Amurka ya yi cewa akwai yiwuwar ɗaliban da aka sace a jihar mabiya addinin Kirista ne. Shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, inda lamarin ya faru, Hon Hussaini Bena, ya tabbatar da cewa dukkanin ƴan matan da aka sace, da mai gadin makarantar da aka harbe duk Musulmai ne. A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, ɗan majalisar Amurkar Riley Moore ya buƙaci magoya bayansa su taya shi yi wa ƴan matan da aka sace da mutumin da aka kashe addu'a. A cewarsa '' duk da ba mu da cikakken bayani game da lamarin, amma mun san an kai harin ne a wani yanki da ke da kiristoci da yawa a Arewacin Najeriya, wajibi ne gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen wannan zaluncin''. A ranar Litinin da asuba ne wasu ƴanbindiga riƙe d...
Na umurci jami’an tsaro su gaggauta dawo da ƴan matan Kebbi – Tinubu

Na umurci jami’an tsaro su gaggauta dawo da ƴan matan Kebbi – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce yana takaicin sace ƴan matan da aka yi a Kebbi, da kuma alhinin mutuwar Birgadiya Janar Musa Uba da gwarazan sojojin da suka mutu a jihar Borno. A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce ya shiga matuƙar damuwa kan mutuwar sojojin ƙasar da ke bakin aiki. Ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da kuma saƙon jaje da iyayen ɗaliban da aka sace, inda ya ce yana ci gaba da yi musu addua. '' Ina cikin damuwa sosai kan yadda ƴan bindiga suka katse wa ƴan matan nan karatunsu, na umurci jam'ian tsaro su yi gaggawar dawo da ƴan matan gida'' '' Ina sane da ƙaruwar rashin tsaro a wasu sassan ƙasar, kuma na bai wa jami'an tsaro umurnin daƙile matsalolin cikin gaggawa''. a cewar shugaban. Ya kuma yi kira ga ƴan ƙa...
Allah Sarki: Karanta Jadawalin Manyan Sojojin da suka rhasa Rhayuwkansu a Fagen daga

Allah Sarki: Karanta Jadawalin Manyan Sojojin da suka rhasa Rhayuwkansu a Fagen daga

Duk Labarai
A ranar Talata ne rahotonni suka fara ɓulla cewa mayaƙan ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (Iswap) ta kashe Birgediya Janar Musa Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Kisan nasa ya tayar da muhawara game da yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap ke kashe manyan jami'an sojin Najeriya, duk da cewa ba shi ne na farko da ya mutu a filin daga ba. Bayanai sun nuna cewa Janar Uba ne babban jami'i na biyu mafi girman muƙami da 'yanbindigar suka kashe tun shekarar 2021. Iswap ta bayar da sanarwar kisansa a shafinta na Telegram, inda ta ce mayaƙanta sun kama shi ranar 15 ga watan Nuwamba bayan harin kwanton-ɓauna da suka kai wa sojojin Najeriya a kusa da garin Wajiroko da ke jihar ta Borno. Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da kai h...
Rahoto: Rashin aikin yi a tsakanin Matasan Qasar Amurka yayi Qamari, babu banbanci tsakanin masu Digiri da wadanda basu je makaranta ba

Rahoto: Rashin aikin yi a tsakanin Matasan Qasar Amurka yayi Qamari, babu banbanci tsakanin masu Digiri da wadanda basu je makaranta ba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar Amurka yayi Qamari. Rahoton wanda gidan jaridar Fortune ya wallafa yace a tsakanin matasa masu shekaru tsakanin 22 zuwa 27, rashin aikin yin su iri daya ne, babu banbanci tsakanin wanda yaje makaranta da wanda bai kammala Digiri ba. Rahoton yace rashin aikin yi a tsakanin matasan ya kai makin kaso 5.5 cikin 100. Rahoton yace kamfanoni da yawa da masu daukar aiki sun rage baiwa kwalin Digiri muhimmanci. Hakan yasa matasa suka fara barin karatun Digiri suna komawa makarantun koyon sana'a.
Doka ta bani dama zan iya kwace fili daga hannu kowanene sannan in baiwa wanda nake so a Abuja>>Inji Wike

Doka ta bani dama zan iya kwace fili daga hannu kowanene sannan in baiwa wanda nake so a Abuja>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan Babbban Birnin Tarayya, Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa, doka ta bashi damar kwacewa da baiwa kowa yake so fili. Ya bayyana hakane yayin ziyarar da shuwagabannin hukumar kula da yankin kudu maso kudu suka kai masa. Yace idan mutum ya bar filinsa ba tare da ginawa ba na tsawon lokaci, ko kuma ya ki biyan haraji ko ya saba doka zai iya kwace filinsa. Wike yace baya kwace fili saboda siyasa yace abin takaici ne ace mutane basa son biyan Haraji amma suna son gwamnati ta rika musu aikin gina kasa.
Kalli Bidiyo: Amsar da Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta bauwa wani da yace mata Timaya ya hama Qakuleta

Kalli Bidiyo: Amsar da Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta bauwa wani da yace mata Timaya ya hama Qakuleta

Duk Labarai
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta wallafa Bidiyo a shafinta na Tiktok tana sauraren wakar Aliya inda anan ne wani ya bayyana cewa Timaya ya gama kwakuleta. Saidai maimakon ta ji haushi, Ummi ta gaya masa cewa, zaka maimaita Ranar Sakamko ai. https://www.tiktok.com/@ummi_zee_zee_offi/video/7573076778344828167?_t=ZS-91XCE153d3Z&_r=1 Ummi Zeezee dai ta yi soyayya da mawakin Kudu, Timaya wanda a wancan shekarun lamarin ya jawo cece-kuce.
Kalli Bidiyon yanda matashi ya fito yana zanga-zanga shi kadai yana kiran kasar Amurka ta kawo dauki Najeriya inda yace shuwagabanni sun gaza

Kalli Bidiyon yanda matashi ya fito yana zanga-zanga shi kadai yana kiran kasar Amurka ta kawo dauki Najeriya inda yace shuwagabanni sun gaza

Duk Labarai
Wani matashi kenan da ya fito a Abuja yana zanga-zanga shi kadai yana cewa, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kawo dauki Najeriya. An ga matashin a Bidiyo yana daga kwali yana durkusawa kasa yana kiran sunan Trump. https://www.tiktok.com/@gabriel__timothy/video/7574103452331134216?_t=ZS-91XAQO7iV8K&_r=1
An gano cewa, Wasu Inyamurai ne masu son kafa kasarsu suka kai Rahoton cewa ana Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya zuwa kasar Amurka

An gano cewa, Wasu Inyamurai ne masu son kafa kasarsu suka kai Rahoton cewa ana Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya zuwa kasar Amurka

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu Inyamurai ne karkashin wata Kungiya ta son kafa kasar Biafra suka kai kara kasar Amurka cewa ana yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi a Najeriya. Rahoton yace kungiyar me suna the United States of Biafra da sauran wasu kungiyoyin dake karkashinta sun mika wannan korafi ne ga Hukumar FARA ta kasar Amurka. Sannan Sanatan kasar Amurka, Ted Cruz ya taimaka musu wajan yayata wannan magana inda yace babu inda akewa Kiristoci Khisan kyiyashi kamar a Najeriya. Lamarin dai ya watsu sosai musamman a kafafen sada zumunta. Saidai Tuni Gwamnati ta musanta wannan rade-radin.