Monday, January 13
Shadow

Lauyayin ciki

Cikin wata hudu

Haihuwa, Lauyayin ciki, Nakuda
Bayan cikinki ya kai wata 4, ga abubuwan dake faruwa: Dan dake cikinki ya kai girman inchi 3 ko ace 8 cm. Za'a iya gane wane jinsi ne abinda ke cikinki saboda za'a iya ganin al'aurarsa a na'urar gwaji ta Ultrasound. Gashin kan abinda ke cikinki ya fara fitowa. An halicci saman baki ko lebe. Da yawa daga cikin Alamomin farko da kika fara ji na daukar ciki zasu daina damunki bayan da cikinki ya kai watanni 4. Saidai matsalolin rashin narkewar abinci zasu iya ci gaba da bayyana a jikinki, kamar wahala wajan yin kashi, zafin kirji ko zuciya. Nononki zai kara girma, zai rika zafi sannan kan nononki zai kara yin baki. Zaki iya samun matsalar numfashi sama-sama ko kuma yinshi da sauri. Dasashin bakinki zai iya yin jini, zaki iya yin habo, watau zubar da jini ta hanci, ...