Tuesday, January 7
Shadow

Kiwon Lafiya

Maganin kara tsawon azzakari

Jima'i
Akwai magunguna na gargajiya da yawa da ake amfani dasu dake ikirarin kara tsawon azzakari, saidai masana kiwon lafiya sun ce babu wani maganin dake kara tsawon Azzakari. Masana kiwon lafiya sun ce hanya daya ce ake kara girman azzakari shine a yiwa mutum tiyata. Hakanan akwai wasu hanya kamar wata na'ura da ake bugawa azzakarin iska kaga ya mike, ko kuma na'ura me janyo azzakarin, saidai shima masana sunce wannan hanya bata cika yin aiki ba. Saidai a lokacin da aka buga iskan, azzakarin zai iya mikewa sosai amma daga baya zai koma yanda yake, wasu suna samun karin girman azzakarin amma ba sosai ba yanda ake tsammani. Saidai duka wadannan maganganu a kimiyyance muke magana, a gargajiyance da al'adu daban-daban mutane da yawa sun yadda zasu iya kara girman azzakarin su ta hanyar s...

Amfanin man zaitun ga azzakari

Amfanin Man Zaitun, Jima'i
Ana alakanta cewa, shafa man zaitun akan mazakuta ko Azzakari yana kara masa girma, saidai a likitance babu wani bincike da ya tabbatar da hakan. Hakanan ana yada cewa, hada man zaitun da albasa yana kara girman azzakari amma shima wannan babu wata hujjar bincike ta masana da suka tabbatar da hakan. Saidai kuma babu wata illa a amfani da man zaitun akan azzakari da masana suka tabbatar, dan haka zaka iya gwadawa a gani ko zai yi aiki. Wani abu da mutane da yawa basu sani ba shine, Yawancin maza azzakarinsu ba karami bane, mutum ne da kanshi zai rika jin kamar bai gamsu da girman azzakarinshi ba har daga nan ya fara neman maganin karin girmansa. Masana sun bayar da shawarar cewa, yana da kyau mutum yayi magana da matarsa yaji shin yana gamsar da ita a yayin jima'i? Idan dai mutu...

Amfanin man zaitun a gaban mace

Amfanin Man Zaitun, Jima'i
Ana amfani da man zaitun a gaban mace dan magance matsalar kaikayin gaba ko kuma ace infection. Ga masu matsalar bushewar gaba, ana iya yin amfani da man zaitun dan magance wannan matsalar. Musamman a yayin jima'i, ana iya amfani da man zaitun a matsayin man da zai karawa ma'aurata jin dadin saduwa. Hakanan ko da mace lafiyarta qalau, wasu bayanai sun nuna cewa, tana iya yin amfani da man zaitun dan rigakafin infection a gabanta. Hakanan masana sunce shafa man zaitun a gaban mace yana rage zafin da mata ke fama dashi a lokacin jinin al'ada. Domin shafa man zaitun a cikin gaban mace, ana iya sakashi akan yatsu biyu a zurasu cikin gaban a shafa.

Amfanin man zaitun da man kwakwa

Amfanin Man Zaitun, Jima'i
Man zaitun da man kwakwa suna da fa'idodi da dama ga lafiya da kyakkyawan jin dadin jiki. Ga wasu daga cikin fa'idodinsu: Amfanin Man Zaitun: Abinci: Man zaitun yana da ma'ana sosai wajen dafa abinci, yana kuma taimakawa wajen rage matakin cholesterol da kuma kare zuciya. Fata: Yana taimakawa wajen sanya fata ta zama mai laushi da kuma rage bushewa. Ana amfani da shi wajen magance kurajen fuska. Gashi: Yana inganta lafiyar gashi, yana hana tsagewa da kuma bushewa. Rigakafin Ciwon Ciki: Man zaitun yana taimakawa wajen rage kumburi a cikin ciki, da kuma inganta narkewar abinci. Amfanin Man Kwakwa: Abinci: Man kwakwa yana da amfani wajen dafa abinci saboda yana dauke da kitse mai kyau wanda yake kara kuzari ga jiki. Fata: Yana taimakawa wajen kula da fata, yana kuma...

Amfanin man kwakwa a gaban mace

Amfanin Kwakwa, Jima'i
Macen da gabanta bashi da ruwa ko baya kawo ruwa, yana bushewa, musamman a lokacin jima'i tana iya amfani da man kwakwa. Man kwakwa inji masaana yana hana bushewar gaban mace. Hakanan a wani kaulin, Man kwakwa yana sa hasken gaban mace. Ana shafashi shi kadai, ko kuma domin samun sakamako me kyau, a hada da ruwan lemun tsami a shafa, yana sa gaban mace yayi haske. Hakanan man kwakwa yana maganin kaikayin gaba dake damun mata ko kuma ace infection. Ana shafa man kwakwa a gaba dan magance yawan kaikai dake sa susa a ko da yaushe. Ana iya shafashi a saman gaban mace ko kuma a shafashi a cikin gaban, duk yana magani. Hakanan bincike ya nuna cewa,Man kwakwa na taimakawa mata masu fama da matsalar yoyon fitsari.

Amfanin man kwakwa a nono

Amfanin Kwakwa, Nono
Bincike ya tabbatar da man Kwa na maganin bushewa ko tsagewar kan nono. Ana shafa man kwakwa akan nono da yake bushewa ko ya tsage dan dawo dashi daidai. Hakanan idan kan nono yana zafi ko yana ciwo,shima bincike ya tabbatar da cewa, ana shafa man kwakwa kuma ana samun sauki da yardar Allah. Kuma idan kan nono yana kaikai, shima ana shafa man kwakwa dan magance wannan matsala. Hakanan wasu bayanai sun ce shafa man kwakwa akan nono yana batar da nankarwa da karawa nonon lafiya. Hakanan wasu bayanai sunce ana amfani da man kwakwa wajan sanya kan nono yayi haske, saidai bayanin yace sai an dauki lokaci kamar wata 2 ana shafawa kamin a samu sakamako me kyau. Hakanan wasu bayanai da ba'a tabbatar dasu ba sun ce shafa man kwakwa yana tayar da nonuwan da suka zube. Ana iya gwad...

Ya mace take gane tanada ciki

Gwajin Ciki
Babbar hanyar da mace take gane tana da ciki shine ta hanyar gwaji. Akwai hanyoyin gwaji da yawa amma mafi inganci itace zuwa Asibiti ko kuma amfani da tsinken gwaji wanda ake kira da pt strip test a gida. Ana iya samun tsinken gwaji a kemis da yawa kuma bashi da tsada, saidai dan samun sakamako mafi kyawu a bari sai bayan kwanaki 10 ko 14 a kamin ayi gwajin cikin bayan yin jima'i, wasu masana ma na cewa a bari sai bayan kwanaki 21 kamin a yi gwajin cikin. Inda wasu kuma ke cewa a bari sai bayan an yi batan wata, watau idan lokacin zuwan jinin al'ada yayi amma ba'a ganshi ba. Ana kuma amfani da hanyoyin gargajiya da yawa wajan gwajin ciki kamar amfani da gishiri, suga, da sauransu amma dai yin amfani da tsinken gwaji yafi tabbas ko kuma aje asibiti. Akwai alamun shigar ciki...

Menene maganin dadewa ana jima’i

Jima'i
Akwai magunguna da yawa da ake amfani dasu dan a dade ana jima'i. Ga wasu daga cikinsu kamar haka: Cin Ayu, Dodon kodi da sauransu: Masana sunce cin irin wadannan kayan ruwan na taimakawa mutum ya samu karfin yin jima'i. Shan Chakulan, ko Chocolate: Masana sun ce shan alawan Chakulan na taimakawa matuka wajan baiwa namiji kuzari. Kankaka: Masana sun ce shan kankana yana taimakawa namiji sosai wajan samun kuzari da gamsar da iyali. Ayaba: Masana sun tabbatar da cewa cin Ayaba yana taimakawa namiji ya samu kuzari sosai yayin kwanciya da iyali. Cin Kifi, Musamman Sardines yana taimakawa namiji sosai wajan samun kuzarin kwanciya da iyali. Masana sun ce domin samun dadewa ana jima'i da gamsuwa: A daina saka kai damuwa sosai. A daina shan giya. A daina shan Taba. ...

Maganin dadewa ana jima i na bature

Jima'i
Akwai magunguna da yawa da ake amfani dasu wajan sa maniyyin mutum ya dade bai kawo ba yayin jima'i. Hakan zai sa mutum ya dade yana yi ba tare da gajiya ba. Akwai na Hausa Akwai na turawa, anan kasa mun kawo muku na turawa wanda ke taimakawa ana dadewa ana jima'i: Akwai sanannen wanda ake cewa Viagra, wannan masana sun ce ana shanshine kamin a ci abinci. Kuma yana fara aiki ne mintuna 30 bayan an shashi. Sannan yana aiki a jikin mutum na tsawon awanni 4 zuwa 6. Akwai kuma wanda ake cewa Cialis wannan shima yana fara aiki mintuna 30 bayan an shashi saidai yana da karfi sosai dan yana kaiwa kusan kwana biyu yana aiki, shiyasa masana ke bayar da shawarar a shashi a karshen mako. Akwai kuma Levitra wanda ke aiki kamar Viagra. Akwai kuma Spedra wanda shi kuma yana aiki ne min...

Yadda ake kamuwa da ciwon hanta

Ciwon hanta
Ana kamuwa da ciwon hantane ta hanyar abinda ake cewa Virus, saidai wasu kalolin abinci, irin su giya, shan maganin gargajiya, da shan hadin gambizar magungunan asibiti ba tare da umarnin likita ba suma suna kawo cutar hanta. Shan abubuwan zaki na leda ko na roba wanda aka sarrafa suma suna iya haifar da cutar hanta. Hakanan yawan cin soyayyen abinci shima na iya haifar da cutar hanta. Hakanan wasu ana haihuwarsu da cutar ta hanta. Wannan virus na cutar hanta na yaduwa ne ta hanyar maniyyi, ruwa, abinci marar kyau, yin ma'amala ta kusa da wanda ya kamu ko ta hanyar jini. Saidai ita wannan cuta idan bata yi tsanani ba ana iya warkewa. Kuma akwai hanyoyi da ake bi wanda idan Allah ake inganta lafiyar hantar. Allah ya karemu da lafiya. Amin.