Friday, October 4
Shadow

Gashin gaba

Gashin Gaba ko kuma ace gashin mara gashine dake fitowa a jikin farjin mace da kuma azzakarin namiji wanda alamace dake nuna cewa mutum ya fara girma kuma ya balaga kuma hukuncin shari’a ya hau kansa.

Tsaftace gashin gaba yana da muhimmanci dan yana sakawa mutum ya rika samun nutsuwa sannan kuma yana taimakawa wajan hana warin gaba.

Yana da kyau a aske gashin gaba, ko da ba’a aske duka ga, a rika rage masa tsawo daga lokaci zuwa lokaci.

Sannan kuma idan an barshi a rika wankeshi akai-akai dan idan ba’a kula dashi za’a ga ya kan rika daukar datti ya canja kala ya koma ruwan kasa, har ya rika wari.

Karanta Wannan  Amfanin toka a hammata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *