Friday, December 5
Shadow

Cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘Yanci: Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutu ranar Laraba

Gwamnatin Najeriya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai.

Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”.

Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960.

A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yansanda sun kama 'yan kasar China 80 suna ayyukan damfarar yanar gizo a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *