
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayarwa da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Datti Baba Ahmad martani bayan da yace idan shugaban kasar na da wayau kada ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 saboda faduwa zabe zai yi.
A martaninsa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace maganar Datti ta banza ce wadda ba basira ko kadan a ciki.
Da yake magana da bakin kakakinsa, Daniel Bwala, Shugaba Tinubu yace Datti Ahmad ya daina shiga harkar da bai iya ba, watau siyasa, ya barwa wanda suka iya su yi.
Yace yayi kokari sosai na daukar matakan gyara wanda ‘yan Najeriya sun shaida kuma har kungiyoyin Duniya irin su IMF sun jinjina masa inda suka ce ya Dora Najeriya a turbar karfafa tattalin arziki.