Monday, December 16
Shadow

Cin bashin da ƴan Najeriya ke yi ya ƙaru saboda matsin rayuwa – CBN

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da rahoton cewa, ƴan Najeriya sun koma cin bashi daga bankuna da manhajojin karɓar bashi saboda tsananin tsadar rayuwa domin samun biyan buƙata.

CBN ya ce an samu ƙaruwar masu ciyo bashi da kashi 12 cikin 100, inda ya kai kusan tiriliyan ₦3.9 a watan Janairun 2024.

An danganta wannan ƙaruwar ciyo bashin da hauhawar farashin kayan masarufi.

Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ruwaito cewa hauhawar farashin kaya ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu.

Hakan ya sa babban bankin ƙasar ya ƙara yawan kuɗin ruwa a jere zuwa kashi 26.25 bisa 100.

Hauhawar farashin kaya ya jefa ƴan Najeriya cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya ƙara tsadar rayuwa.

Karanta Wannan  YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

Wani bincike da SBM Intelligence ya gudanar ya nuna cewa kashi 27 cikin 100 na ‘yan Najeriya masu yawan samun kudin shiga daban-daban a yanzu sun dogara ne ga manhajojin ƙarbar bashi domin gudanar da abubuwan rayuwa yayin da ake fama da hauhawar farashin kaya.

Ƙaruwar buƙatun ciyo bashi ta hanyar manhajar ƙarbar bashi ko kuma daga bankuna yana nuna tsananin tasirin hauhawar farashin kaya ga ƴan Najeriya, musamman waɗanda ke da ƙarancin kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *