Friday, February 7
Shadow

Coci a jihar Delta ta kori Reverend Fr. Daniel Okanatotor saboda ya je kasar Amurka yayi aure a boye wanda a dokar kiristanci bashi ba aure tunda ya kai mukamin Priest

Coci a jihar Delta ta dakatar da Fr. Daniel Okanatotor saboda zuwa kasar Amurka yayi aure a boye wanda a dokar kiristanci tunda ya kai matsayin Priest, to bashi ba aure har ya mutu.

Cocin me suna The Catholic Diocese of Warri ta sanar da cewa ta dakatar da Fr. Daniel daga mukamin Priest a wata sanarwa data fitar ranar 16 ga watan Janairu

Tace Fr. Daniel ya sanar da ita cewa zai ajiye mukamin na Priest, saidai tace kamin ta kammala sauke masa mukamin, sai kawai ta ji labarin yayi aure.

Dan haka ne ta sanar da dakatar dashi.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: Harajin da ƴan Nijeriya ke biya ya yi kadan – Bill Gates

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *