Monday, December 16
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Cika Hannu Da Kwamishinaɲ Jihar Jigawa yana tsaka da Làląta Da Mątar Aúrê

Biyo bayan wani sumame da ta kai dangane da bayanan da ta samu, hukumar (HISBAH) ta Jihar Kano ta yi ram! Da kwamishinan ayyuka na musamman na Jihar Jigawa, Auwal Ɗalladi Sankara, a bisa zargin láląta da mátar aúré.

A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, mijin matar ne ya shigar da ƙara a gaban hukumar yana tuhumar kwamishinan da yin tarayya da matar tasa wanda hakan ya sanya hukumar yi masa ƙofar rago tare da kama shi.

Majiya daga Jaridar Daily Nigerian da Sahara Reporters sun tabbatar da cewa yanzu haka kwamishinan yana tsare a hedikwatar hukumar ta (HISBAH) da ke Kano tun daren jiya Alhamis bayan kama shin, wanda kuma bayan kammala bincike ne za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Farashin litar man fetur ya kai Naira 937 a jihar Jigawa

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *