Friday, December 5
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Karon Farko Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani

DA ƊUMI-ƊUMI: Karon Farko Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani.

Rahotanni da ke shigo mana yanzu sun tabbatar da cewa Nijeriya za ta karɓi bakwancin masabaƙar karatun Alkur’ani mai girma ta duniya a wannan shekarar.

Majiyar Jaridar Arewa ta tabbatar da cewa Musabaƙar ta ƙasa da ƙasa wadda za a gabatar a watan Agustan bana 2025.

Tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bassa a Jihar Filato, Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shirya wannan gasar. Hakazalika za a fara daga Jos ne, daga bisani a kammala a birnin Abuja.

Ana kyautata zaton Musabaƙar zata samu halartar wakilai daga ƙasashe kusan 20, na sassan faɗin duniya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Sheikh Salihu Zaria da Shahararren me watsa labarai na Tiktok Sultan suka hadu bayan an sakoshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *