Monday, March 24
Shadow

Ramadan: Coci ya raba wa musulmi kayan abinci a Kaduna

Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry da ke unguwar Sabon Tasha a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ya raba wa musulmi masu ƙananan ƙarfi da makarantun addinin musulunci kayan abinci domin su samu abin sakawa a bakin salati a lokacin azumi.

Shugaban coci, Fasto Yohanna Buru ne ya jagoranci raba kayan abincin, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin musulmi da kirista.

“Muna mayar da biki ne kan yadda Hajiya Ramatu Tijjani take yawan ba kirista kayan abinci a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara,” in ji shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Karanta Wannan  Sojoji sun ce sun lalata sansanin Bello Tùrjì tare da kkashe 'yànbìndìgà 25

Fasto Buru ya ce suna da burin tallafa wa aƙalla mutum 1,000 ne a azumin na bana, sannan ya ce ya jagoranci haɗa malamai da fastoci aƙalla guda 30 domin gangamin jawo hankalin ƴan kasuwa game da muhammancin rage farashin kayan abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *