Wednesday, January 15
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

Cire harajin ya shafi kayan asibiti da suka haɗa da magunguna na ƙwayoyi da na ruwa, sirinji da allurai, sanke na rigakafin cizon sauro, abubuwan gwaji na gaggawa, da sauran kayan amfani a asibiti na yau da kullum.

Hakazalika, umarnin na shugaban ƙasa zai ƙara ƙarfafawa masana’antun sarrafa magunguna da kayan asibiti na cikin gida wajen kara inganta su da samar da su a wadace.

Wannan zai rage farashin magunguna da kuma wadatar su a lunguna da saƙon kasar nan don amfanin ƴan Najeriya.

Karanta Wannan  An kashe jimullar Mutane 4,416 sannan an yi garkuwa da 4,334 a shekara 1 da Tinubu yayi yana mulkin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *