
Hùkumar Hisba Ta Haramta Çàça, Dara Da Wasan Ĺìdo Da Ake Bugawa A Wayoyin Hannu A Garin Dutsin-ma Na Jihar Katsina
Daga Comr Nura Siniya
Hukumar Hisbah reshen karamar hukumar Dutsin-ma a jihar Katsina ta saka dokar hana caca da wasan lido a majalissun gari da sauran wuraren masha’a domin yaki da ayyukan badala a karamar hukumar ta Dutsin-ma da ma jihar Katsina baki ɗaya.
Haka zalika Hisba ta haramta dara da wasan karta da aka fi sani da “Whot wanda ake bugawa a wayoyin hannu da kasuwanni.
Hukumar ta gargadi jama’a da su kiyaye idan ba haka ba za su fuskanci fushin hukuma.