
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Labour party, Datti Ahamad ya bayyana cewa, da dai ace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na da wayau, da ya hakura da tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
Ya bayyan hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda yace dukkan alamu sun bayyana cewa, jam’iyyar APC faduwa zata yi.
Yace kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai cikawa ‘yan Najeriya alkawuran da ya dauka ba.
Yace Buhari bai cika alkawuran da ya dauka ba saboda APC makaryaciyar jam’iyya ce.