DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu.
Abin jira dai a gani shine ko ‘yansandan zasu bi umarnin Kotun, ganin cewa a baya ma an samu wata kotu ta bayar da umarnin hana sauke Aminu Ado Bayero amma umarnin bai yi amfani ba?
Rigimar sarautar Kano dai ta dauki hankula sosai a kasarnan inda a karon farko aka samu sarakuna biyu a jihar da kowane ke cewa shine sarkin Kano.