DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai.
Al’amarin dai ya faru ne a garin Ɗanmarke da ke karƙashin ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara, a ranar Larabar nan da daddare, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ƴansandan jihar ta Zamfara ta fitar.
Dpon an tsaida shi a checkpoint na dan marke da ke cikin Karama Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara ya ki tsayawa, wanda hakan yasa sojoji suka yi waya gaba domin su rufe hanya ga mota nan zuwa mai kala kaza, ga sunan zuwa.
Nan da nan suka bi umurnin soji nan take sojoji su ka biyo motarsa yana zuwa ya isko an rufe hanya, bayan ya bayyana kan sa matsayin ɗan sanda ne, sai kuma ya fita daga motar zai gudu wanda hakan yasa sojojin suka bude masa wuta.
Daga bisani aka fara binciken motar sa sai ga bindigogi guda biyu kirar Ak47 da zai shiga dasu zuwa jihar Zamfara, kuma a jihar Kebbi ya ke aiki.
SP Halliru Liman wanda shi ne DPO na Wasugu da ke jihar Kebbi ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa ta halartar taronsu na wata-wata, inda sojoji suka tsayar da shi a wani shingen bincike.