Friday, December 5
Shadow

DA DUMI DUMINSA: Ni Zan jagoranci Al’ummar jihar Kano Mu kayar da Gwamnatin kwankwasiyya a 2027, Kwankwaso ba zai iya cin Zaɓen Gwamna a jihar Kano Ba, Sannan Ba Zai kai labari ba a Kano balle a Najeriya- Dr Baffa Bichi

cikin wata hira da akayi dashi a gidan radio Rahma dake jihar Kano Dr Baffa Bichi ya ce ba wannan ne karon farko da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake tsayawa takara amma yake gaza yin nasara ba.

’’Kwankwaso yayi takarar shugaban kasa a jam’iyar APC bayyi nasara ba yayi a jam’iyar PDP nan ma bayyi nasara ba a shekara ta 2019 da temakon Atiku Abubakar, yayi takara don yayi nasara a jihar Kano amma dashi da Atiku suka fadi ko karamar hukumar sa ta kwankwaso bai kawo ba.

Ya ce a lokacin da Kwankwaso yayi hadaka da Atiku Abubakar bayyia nasara ba ta yaya a yanzu da ya koma sabuwar jam’iya shi kadai zayyi hakan ba zai taba yiwu ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Naje kasar waje karbi iPhone amma abinda aka ce za'a yi dani kamin a bani wayar yayi muni shiyasa naki yadda>>Inji Bashir Gombe

Dr Baffa Bichi ya kara da cewa la’akari da bangaranci da son kai na Kwankwaso da kuma kasancewar Atiku Abubakar yana takara a yanzu wannan wata dama ce ga Jam’iyar Apc a jihar Kano tayin nasara a zaben 2027

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *