DA DUMIDUMINSA: Muna Tare Da Tinubu Dari-Bisa Dari, Inji Tsoffin Membobin Tsohuwar Jam’iyyar CPC Magoya Bayan Buhari

Magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karkashin kungiyar tsohuwar jam’iyyar CPC dake cikin jam’iyyar mai mulki ta APC, wanda Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya jagoranci hira da manema labarai a yau Alhamis sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis.
Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar ba sa jin dadin yadda Tinubu ke tafiyar da al’amura, kuma suna shirin ficewa daga jam’iyyar APC gaba ɗaya.
Cikin wadanda suka halarci taron a Abuja ranar Alhamis, wadanda kuma suka nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Tinubu, akwai Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Radda; wakilin Gwamnan jihar Neja, Umar Bago; tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Almakura; tsohon Gwamnan jihar Katsina kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Aminu Bello Masari da Shugaban Hukumar NDLEA, Janar Buba Marwa (ritaya).
Sauran sun hada da tsohon Darakta Janar na Voice of Nigeria (VoN), Osita Okechukwu; tsohon mataimakin shugaban kasa a fannin shari’a, Okoi Obono Obla; tsohon Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Arc. Waziri Bulama; tsohon dan Majalisar Wakilai, Farouk Adamu; wakilin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas da Ministan Harkokin Waje, Maitama Tuggar da wasu da dama.
Sun bayyana cewa kowane mutum yana da ’yancin bin muradinsa na siyasa a duk inda ya ga dama, amma ba sai an yi hakan da sunan “mambobin tsohuwar jam’iyyar CPC” ba.
Yayin da aka tambayi ko wannan kungiya za ta ci gaba da mara wa Tinubu baya, daya daga cikin shugabanninta, Hon. Farouk Adamu, ya bayyana kyakkyawar fata cewa Tinubu zai ci gaba da zama dan takararsu a shekarar 2027.
“Mun tsaya tare da Tinubu kamar yadda shugabanninmu (Buhari) ke tare da shi, kuma muna fatan zai ci gaba da zama shugabanninmu,” in ji shi.