A karin farko a shekarar 2025, wutar lantarkin Najeriya ta samu tangarda. Hakan na zuwane yayin da ake kwanaki 11 da shiga sabuwar shekara.
Lamarin ya kawo daukewar wutar lantarki wanda hakan ya jefa mutane da yawa cikin duhu a Najeriya.
Hukumomin dake kula da wutar lantarkin sun tabbatar da tangardar wutar inda sukace aka kan kokarin gyarata.