
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya maka shugaban Hukumar MNDPRA, Engnr. Farouk Ahmed ga hukumar ICPC inda yace yana zarginsa da satar kudin talakawa.
Dangote yace Ahmad yayi amfani da dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta a kasar Switzerland.
Dangote yace gaba daya rayuwar Ahmad yayi ta ne a matsayin ma’aikacin gwamnati kuma idan aka tattara kudin albashinsa da alawus ko kusa ba zasu kai dala Miliyan $7 ba.
Yace dan haka yana amfanine da hukumar da yake shugabanta wajan karkatar da kudaden Talakawa kawai.
Dan Haka Dangote yace yana neman hukumar ta ICPC ta bincikesa.
Dangote ya bayyana hakane ta hanyar lauyansa, Ogwu Onoja (SAN) ranar 16 ga watan Disamba.