
A zaman majalisar tarayya na yau, Alhamis, majalisar ta dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6.
Tun farko dai shugaban kwamitin ladaftarwa na majalisar, Sanata Neda Imasuen ne ya bayar da shawarar dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 sannan a dakatar da albashinta da kuma janye jami’an tsaron dake bata kariya.
Yace ya kamata a dauki wannan mataki ne saboda sanata Sanata Natasha Akpoti ta karya dokokin majalisar sannan an gayyaceta zuwa gaban kwamitin ladaftarwa saidai ta ki amsa gayyatar.
A karshe dai majalisar ta amince da dakatar da sanata Sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 sannan kuma jami’an tsaro sun tasa keyarta zuwa waje.
Saidai kamin ta fita tace wannan rashin adalcin ba zai dore ba.