
Rahotanni daga babban birnin kasar Amurka, Washington DC na cewa an kashe ma’aikatan ofishin jakadancin kasar Israela 2.
An bayyana lamarin da cewa Kiyayya ce ga Yahudawa.
Wani rahoto yace maharbin yayi ihun cewa a kyale Falasdinawa kamij ya kashe mutanen.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana Allah wadai da lamarin inda yace irin wannan lamari bashi da mazauni a kasarsu.