Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: An sake daga jana’izar Aminu Dantata

Bayanai daga makusantan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata sun nuna cewa an ɗage jana’izar marigayin da aka shirya gudanarwa bayan sallar La’asar a ranar Talata.

Yanzu an mayar da jana’izar zuwa bayan Magariba a haramin birnin Madina.

Dama dai Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya shaida wa BBC cewa tuni gawar Alhaji Aminu ta isa birnin na Madina.

“Alhamdu lillah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya shi kafin daga bisani a kai shi haramin Madina domin gudanar da sallah kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince.” In ji Mustapha Junaid.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu Ya Isa Kasar Saudiyya Domin Sasanta Riķiçin Gabas Ta Tsakiya

A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *