
Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutanene sun sace dansandan Najeriya da wasu mutane.
Rahoton yace an sace CSP Modestus Ojiebe ne akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Dansandan dake aiki a Kwara an yi garkuwa dashine a lokacin da yake kokarin gyaran motarsa da ta lalace a kusa da barikin ‘yansanda dake Dei-Dei.
Rahoton yace wata motace ta je kusa dashi ta yi fakin inda mutane dauke da makamai su 4 suka fito daga cikinta suka kwace mai wayoyinsa dana matarsa, saidai da suka ga shaidar katin aikin dansanda, sun yi garkuwa dashi inda suka jefashi cikin mota suka tafi dashi.
Tuni dai aka saka jami’an tsaro a hanyoyin shiga da fita birnin Abuja.
Wasu ‘yansanda sun tabbatar wa da Jaridar Daily Trust da wannan labari saidai har yanzu hukumomin ‘yansandan na Abuja da Kwara basu fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba.