Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: APC ta yi magana kan komawar Kwankwaso jam’iyyar

Jam’iyyar APC ta yi magana kan rade-radin dake jawo cewa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar.

Hakan na zuwane bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC inda ake ta samun rahotannin cewa, yanzu Kwankwaso zai koma jam’iyyar.

Me magana da yawun jam’iyyar APC a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV yace babu wannan maganar.

Yace bai san komai ba game da rahotannin dake yawo cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC ba.

A wasu rahotannin dai har cewa aka yi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai dauki Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.

Karanta Wannan  Zan koma jam'iyyar APC duk wanda ba zai biyo ni ba sai ya ajiye mukamin dana bashi ya kara gaba>>Inji Gwamnan Jihar Akwa-Ibom

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *