
Rahotanni daga jihar Abia na cewa, ‘yan Bindiga sun budewa motar kwamishinan gidaje na jihar, Mr. Chaka Chukwumerije wuta inda suka fasa gilasan motar.
Lamarin ya farune da daren ranar Asabar akan titin Enugu-Umuahia dake jihar Imo.
Rahotanni sun ce lamarin ya farune a yayin da dan siyasar ya baro mahaifarsa, Umunneochi yana kan hanyar zuwa Umuahia.
Akwai mutane 3 da suka rakashi saidai babu wanda ya jikkata a harin amma motarsu ta lalace da harin harsashi.
A jawabinsa bayan faruwar lamarin, Chukwumerije ya bayyana cewa, Allah ne ya tsaresu a harin daya faru inda yace lamarin ya matukar girgizashi.