
Rahotanni daga ma’aikatar noma ta Najeriya ta sanar da dakatar da shirinta na tursasa ma’aikatan ta yin azumin kwanaki 3 dan neman sa’a wajan wadata Najeriya da abinci.
Takardar umarnin daukar azumin ta bayyana inda aka ga cewa an bukaci ma’aikatan hukumar da su tashi da azumi nan da ranar Litinin.
Saidai bayan da Allah wadai yayi yawa, ma’aikatar ta noma ta dakatar da wannan shiri inda tace sai abinda hali yayi .