
Tsohon me magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina yace da Buhari asibitin Najeriya yake zuwa neman magani, da ya dade da mutuwa.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV da akw tattaunawa dashi game da rasuwar tsohon shugaban kasar.
Femi Adesina yace masu sukar zuwan Buhari asibitin landan ya kamata su fahimci cewa tin kamin ya zama shugaban kasa a shekarar 2015 dama landan yake zuwa ganin likita.
Yace Likitocin na Ingila sun riga sun san tarihin lafiyar tsohon shugaban kasar dan haka babu amfanin a canjasu.
Adesina yace wasu Asibitocin Najeriya basu da kayan aiki da kwarewar da zasu iya kulawa da rashin lafiyar ta Buhari.