Rahotannin da muke samu na cewa, fadar shugaban kasa ta musanta wasu bayanai dake cewa ministan kudi ya gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Naira Dubu dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi.
Babban me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta.
Ga sakonsa kamar haka:
“The Honorable Minister of Finance and coordinating minister of the economy, Wale Edun has not proposed N105,000 minimum wage. The contrary story being disseminated is false.”