
Rahotanni daga Abuja na cewa, gini me hawa 3 ya rushe a Life Camp da ammacin ranar Asabar.
Tini ‘yansanda suka je wajan aka killaceshi sannn hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta kai dauki.
Kakakin ‘yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace an ceto wani dan kasar Nijar a lamarin.
Rahoton yace shi kadai ne lamarin ya rutsa dashi kuma an garzaya dashi asibitin Cedar Crest Hospital inda ake bashi kulawa.