
Wani me sharhi akan al’amuran yau da kullun, Adekunle Adebayo, ya kwarmata cewa Gwamnati na shirin kama tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Hakanan tana son kama Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.
Adekunle Adebayo ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya aikewa jaridar DailyPost ya bayyana cewa wannan shirine na dakile ‘yan Adawa da samar da jam’iyyar siyasa kwaya daya tilo a Najeriya.
Sauran wadanda ya ce za’a kama sun hada da Isa Ali Pantami, Rauf Aregbesola, Kashim Ibrahim Imam.
Saidai yace idan aka yi wannan kamen ya sabawa dokar kasa.