Monday, May 26
Shadow

Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Arewacin Najeriya zasu gana a Kaduna saboda tattaunawa matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Rahoton yace hadimin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Misilli ne ya bayyanawa manema labarai na Punchng hakan inda yace gwamnan Gomben shine ya kira wannan taron a matsayinsa na shugaban Gwamnonin Arewan.

Yace idan dai ba an canja ba, a yau, Asabar ne za’a yi wannan taro a Kaduna kuma matsalar tsaron yankin ce babban abinda za’a tattauna.

Karanta Wannan  Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *