
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC ta gayyaci tsohon babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami.
Malami ne da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta.
Ya kuma tabbatar da cewa, zai amsa wannan gayyatar saboda ya yadda da bincike kuma shi dan kasa ne me bin doka.