
Rahotanni daga hukumar NERC wadda itace ke kula da gudanarwar wutar Lantarki a Najeriya sun ce hukumar ta gano kamfanonin rarraba wutar Lantarki na Najeriya, Discos sun zalinci talakawan Najeriya sun karbi kudin wutar da jama’ basu sha ba.
Hukumar tace Kwastomomi 2,021,913 ne lamarin ya shafa.
Kuma ta umarci kanfanonin na Discos su mayarwa da mutane kudaden su.
Yawanci wadanda aka zalunta din basu da mita, Bill ake kai musu.
Yawan kudaden da aka mayarwa mutane sun kai Naira Biliyan N105.05
Kamfanin wutar lantarki na Ikeja, ya mayarwa da mutane 300,079 kudi da suka kai Naira Biliyan 20.95.
Sai kamfanin wutar Lantrki na Abuja, Abuja DisCo wanda ya mayarwa da mutane 300,013 kudin da suka kai naira Biliyan 17.87.
Kamfanin wutar Lantarki na Enugu kuwa, watau Enugu DisCo ya mayarwa da mutane 302,062 Naira Biliyan 11.87 da ya cucesu.
Shi kuwa Kamfanin wutar Lantarki na Fatakwal, Port Harcourt ya mayarwa da mutane Naira Biliyan N14.19 sai kamfanin wutar lantarki na Eko DisCos da ya mayarwa da mutane Naira Biliyan 14.14 da ya cucesu.
Wannan dai ya nuna gazawar kamfanonin rarraba wutar Lantarkin wajan tabbatar da ainahin wutar da mutum ya sha ita yake biya wanda hakan yasa suke zaluntar mutane.