
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta gargadi mutane akan kada su sayi Taliyar Indomie Vegetable Flavour noodles.
Dalili kuwa shine an gano wani sinadari a cikinta da ka iya yiwa Lafiyar Mutane illa.
Kamfanin Taliyar, ya bayar da umarnin ‘yan kasuwa da suka sayeta su mayar da ita zuwa wajansu.
Kamfanin dake yin taliyar, Rappel Conso of France ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Hukumar NAFDAC tace an gano sinadarin ne bayan kai taliyar dakin bincike.