
Hukumar ‘yansandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da wasu ‘yan APC 6 su gurfana a gabanta dan amsa tambayoyi.
A takardar data fitar yau September 4, 2025 hukumar ‘yansandan tace jam’iyyar ADC ta gabatar mata da El-Rufai da wasu mutane 6.
Ta zargesu da hannu wajan tunzura mutane da kuma kawo hargitsi a jihar.
Sauran wadanda aka gayyata tare da El-Rufai sune Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed, Nasiru Maikano, Aminu Abita, da Ahmed Rufa’i Hussaini