
Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a Karo na biyu.
A ranar Lahadi ne baturen zabe, Farfesa Edogah Omoregie ya bayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 8 ga watan Nuwamba.
Soludo ya samu kuri’u 422,664 sai babban abokin Hamayyarsa, Prince Nicholas na APC ya samu kuri’u 99,445.