Friday, December 26
Shadow

Da Duminsa: Jami’an tsaro sun dira a gidan tsohon Karamin Ministan Mai a lokacin Buhari, Timipre Sylva wanda ake zargin na da hannu a yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Rahotanni sun ce jami’an soji sun kai samame gidan tsohon Ministan man fetur a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Timipre Sylva dake Abuja.

Rahoton na Sahara reporters yace jami’an tsaron sun yiwa gidan kacha-kacha inda suka kuma tafi da wani dan uwan tsohon Ministan.

Rahoton yace Ministan tuni ya bar Najeriya tunda aka fara mai wadannan zarge-zargen.

Hakanan Rahoton yace an kuma kaiwa gidansa na Bayelsa samame.

A baya dai an bayyana cewa akwai wani tsohon gwamnan Najeriya wanda shine ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *