Wednesday, April 29
Shadow

Da Duminsa: Jami’an tsaro sun dira a gidan tsohon Karamin Ministan Mai a lokacin Buhari, Timipre Sylva wanda ake zargin na da hannu a yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Rahotanni sun ce jami’an soji sun kai samame gidan tsohon Ministan man fetur a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Timipre Sylva dake Abuja.

Rahoton na Sahara reporters yace jami’an tsaron sun yiwa gidan kacha-kacha inda suka kuma tafi da wani dan uwan tsohon Ministan.

Rahoton yace Ministan tuni ya bar Najeriya tunda aka fara mai wadannan zarge-zargen.

Hakanan Rahoton yace an kuma kaiwa gidansa na Bayelsa samame.

A baya dai an bayyana cewa akwai wani tsohon gwamnan Najeriya wanda shine ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.

Karanta Wannan  Shekaruna 26 a Musulunci amma na yi ridda na koma Kirista saboda Qur'ani ya fadi karamomin Annabi Isa(AS) da yawa wanda bai fada akan sauran Annabawa ba>>Inji Wannan matashiyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *