
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa, jami’an tsaro sun kama rikakken dan Bindiga da ake nema ruwa a Jallo cikin maniyyatan da ake tantance wa.
Sunan wanda aka kama din shine Yahaya Zango wanda jami’an tsaro sun jima da saka sunansa cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Ya je wajan tantance Alhazai inda ya bayar da fasfo dinsa nan kuwa jami’an DSS suka yi ram dashi aka wuce ofis dashi, kamar yanda Jaridar daily Trust ta ruwaito.