
Rahotanni dake fitowa daga Abuja na cewa, jam’iyyar su Atiku, ADC ta sanar da sabon gurin da zata gudanar da taronta.
ADC tace a yanzu sabon gurin taron nata shine Musa ‘Yaradua Centre Abuja da misalin karfe 2 na ranar Yau, Laraba.
Sanarwar ta fito ne daga mataimakin babban sakataren kungiyar, Nkem Ukandu inda ya kara da cewa kowa shine zai dauki nauyin kansa zuwa wajan taron.
Hakan na zuwane bayan da otal din Wells Carlton Hotel ya soke taron na jam’iyyar.