
Rahotanni daga majalisar Dattijai sun tabbatar da cewa, kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau.
Hakan na zuwane bayan da rahotanni suka watsu cewa ya yanke jiki ya fadi an garzaya dashi asibitin kasar Landan.
Akpabio ya koka da matsalar watsuwar labaran karya inda yace suna da wahalar magancewa.
Majalisar dai ta nemi hukumar ofishin me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, NSA su binciki yanda aka yi labarin ya yadu.