
An samu dambarwa a majalisar Dattijai yayin tantance janar Christopher Musa a matsayin Ministan tsaro.
Sanata Sani Musa daga jihar Naija ya nemi a bar Janar Christopher Musa ya wuce kamar yanda aka sabawa ministocin da aka aika majalisar dan a tantancesu.
Yace Janar Musa tsohon sojane sannan kuma duk tambayoyin da suke masa yanzu sun taba masa irinsu a baya dan haka shi a shawarce yana ganin a kyaleshi ya wuce kawai.
Saidai bai samu goyon bayan sauran ‘yan majalisar ba inda suka ce ya kamata a tsaya a masa tambayoyin da suka kamata.