
Kasar Faransa ta Haramta shan taba sigari a bainar jama’a.
Kasar tace ta haramta shan taba a wajan shakatawa dake gabar tekuna da wajan jiran ababen hawa da sauransu.
Tun a baya dai kasar take ta bayyana aniyar son hana shan taba amma sai wannan karin ta samu nasarar aiwatar da aniyarta.
Rahotanni na bayabayannan sun ce akalla mutane miliyan 7 ne ke mutuwa saboda taba sigari a Duniya.