Friday, October 16
Shadow

Son kai irin na Atiku ne yasa na kusa dashi sai kama gabansu suke suna barinshi>>Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, son kai irin na Atiku Abubakar ne yasa mutanen dake kewaye dashi suke watsewa suna barinshi.

Ya bayuana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Lere Olayinka.

Wike ya bayar da misalin Ifeanyi Okowa wanda yawa Atiku takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 amma yanzu ya koma APC.

Sannan Akwai Gbenga Daniel, wanda shine daraktan yakin neman zaben Atiku a shekarar 2019 amma shima ya bar PDP,

Hakanan kuma yace akwai su Udom Emmanuel Umo Eno wanda duk suke nesanta kansu da jam’iyyar PDP.

Wike yace son kaine irin na Atiku ya jawo hakan.

Karanta Wannan  Ni ba irin sakarkarun 'yan siyasar nan bane wanda kawai daga an musu zargin karya sai su sauka daga mukaminsu, Ni ba zan sauka daga kan mukami na ba>>Godswill Akpabio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *