
Rahotanni daga jam’iyyar ADC na cewa rikici ya barke a jam’iyyar kwana daya da komawar su Atiku da El-Rufai da sauran manyan ‘yan Adawa da suk ce sun zabi jam’iyyar a matsayin wadda zasu yi amfani da ita dan yakar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.
Wani bangarene na jam’iyyar ya balle inda suke neman cewa basu yadda da maganar shigowar su Atiku cikin jam’iyyar ba.
Kakakin bangaren jam’iyyar da suka balle, Musa Isa Matara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yace ba’a tuntubi masu ruwa da tsaki na jihohi ba kamin amincewa sa su Atiku a cikin jam’iyyar ba.