
Rahotanni sun ce hukumar sojojin Najeriya ta canjawa manyan sojoji 60 guraren aiki.
Hakan na kunshe a wata sanarwa ne data bayyana a yau 30 ga watan October inda aka ce sojojin su koma sabbin guraren aikin da aka turasu nan da 3 ga watan Nuwamba.
Tun ranar Juma’ar data gabata ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da canjawa manyan sojojin wajan aiki.
Hakan na zuwane bayan bayyanar rahotanni dake cewa an yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.