
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Ya bayyana abinda suka tattauna da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
A yau ne dai aka ga Kwankwaso ya je fadar shugaban kasar inda suka gana.
Da yake magana da manema labarai bayan ganawar tasu, Kwanwaso yace siyasa ce ta kaishi wajan Tinubu.
Sannan ya kara da cewa akwai yiyuwar zasi yi aiki tare shi da Tinubun, saidai bai kara wani cikakken bayani ba akan hakan.
Wannan haduwa ta Tinubu da Kwankwaso na zuwane bayan da ‘yan adawa suka hade a jam’iyyar ADC.