
Rahotanni sun bayyana cewa, kamin komawarsa ADC, Kwankwaso ya bukaci a bashi damar kawo wanda zai yi takarar Gwamnan jihar Kano.
Saidai jam’iyyar ADC tace ya kamata a bari a yi zabe dan baiwa duka masu ra’ayin tsayawa takara bayyana aniyarsu.
Saidai Rahoton yace Kwankwaso ya dage cewa shi dai a bashi damar ya kawo wanda zai tsaya takara. ADC din dai a karshe ta amince masa.
Rahoton wanda ya fito daga kafar the Whistler yace Kwankwaso Nasiru Yusuf Gawuna yake son tsayarwa a ADC ya fuskanci Abba a 2027.