Saturday, June 27
Shadow

Da Duminsa: Kwankwaso ya zabi wanda yake son yayi takarar gwamnan Kano a ADC, kuma jam’iyyar ta amince masa

Rahotanni sun bayyana cewa, kamin komawarsa ADC, Kwankwaso ya bukaci a bashi damar kawo wanda zai yi takarar Gwamnan jihar Kano.

Saidai jam’iyyar ADC tace ya kamata a bari a yi zabe dan baiwa duka masu ra’ayin tsayawa takara bayyana aniyarsu.

Saidai Rahoton yace Kwankwaso ya dage cewa shi dai a bashi damar ya kawo wanda zai tsaya takara. ADC din dai a karshe ta amince masa.

Rahoton wanda ya fito daga kafar the Whistler yace Kwankwaso Nasiru Yusuf Gawuna yake son tsayarwa a ADC ya fuskanci Abba a 2027.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC, ta dakatar da jigilar fasinja daga Kaduna zuwa Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *